Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiAn kauce wa wani hatsarin jirgin sama bayan ƙofar jirgin ta faɗo...

An kauce wa wani hatsarin jirgin sama bayan ƙofar jirgin ta faɗo a Abuja

An kauce wa hatsarin jirgin sama a Abuja ranar Alhamis, bayan ƙofar wani jirgin haya mai zaman kansa mallakin kamfanin Triton Aviation ta faɗo jim kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin Nnamdi Azikiwe.

An kauce wa hatsarin jirgin sama a Abuja ranar Alhamis, bayan ƙofar wani jirgin haya mai zaman kansa mallakin kamfanin Triton Aviation ta faɗo jim kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin Nnamdi Azikiwe.

Jirgin mai lamba T7-SEI yana kan hanyarsa daga Abuja zuwa Legas lokacin da lamarin ya faru. Hakan ya tilasta wa matuƙan jirgin ayyana dokar ta-ɓaci tare da neman taimakon gaggawa.

Bayan haka, masu kula da zirga-zirgar jiragen sama sun umurci jirgin ya koma Abuja domin saukar gaggawa, yayin da jami’an kashe gobara da ma’aikatan lafiya suka shiga shirin ko-ta-kwana.

Rahoton ya nuna cewa jirgin ya sauka lafiya da misalin ƙarfe 4:34 na yamma agogon UTC, mintuna 14 bayan kiran gaggawar. Daga bisani, jami’an filin jirgin suka tabbatar da cewa ƙofar ta ɓace daga jikin jirgin.

A wani bidiyo da ya yaɗu, wasu manoma sun ce sun gano ƙofar a wata gona da ke Abuja. Hukumar NSIB ta tabbatar da faruwar lamarin tare da tura masu bincike domin gano musabbabinsa, yayin da ba a tabbatar da adadin fasinjojin da ke cikin jirgin ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments