Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiJaafar Jaafar, Dan Bello sun shiga jerin masu aikin jarida da ke...

Jaafar Jaafar, Dan Bello sun shiga jerin masu aikin jarida da ke amfanar al’umma

Mawallafin jaridar Daily Nigerian da Daily Nigerian Hausa, Jaafar Jaafar, na cikin ’yan jarida shida da suka samu kyautar girmamawa kan gudummawar da suke bayarwa wajen wayar da kan jama’a da inganta shugabanci nagari a Najeriya.

Mawallafin jaridar Daily Nigerian da Daily Nigerian Hausa, Jaafar Jaafar, na cikin ’yan jarida shida da suka samu kyautar girmamawa kan gudummawar da suke bayarwa wajen wayar da kan jama’a da inganta shugabanci nagari a Najeriya.

Ƙungiyar Patriotic Volunteers for Good Governance ce ta bayar da kyaututtukan a taronta na shekara-shekara da aka gudanar a sakatariyar ƙungiyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Kano, ranar Lahadi.

Sauran waɗanda suka samu kyautar sun haɗa da Dr Habib Bello Galadanci, wanda aka fi sani da Dan Bello; Ibrahim Ishaq Dan Uwa Rano; Salamatu Sabo Bakin Zuwo ta Express Radio Kano; Abbas Salisu Soron Dinki na Rahma Radio Kano; da Abubakar Murtala na Matashiya Radio-TV Online.

Shugaban ƙungiyar, Usman Alhaji, ya ce an ba su kyaututtukan ne saboda gudummawar da suke bayarwa wajen ilimantar da jama’a, ƙarfafa shigar ’yan ƙasa cikin harkokin mulki da kuma bibiyar al’amuran da suka shafi rayuwarsu.

Ya bayyana cewa aikin ’yan jaridan ya taimaka wajen wayar da kan jama’a kan zaɓe, tantance ’yan takara, binciken alkawuran kamfe da kuma jawo hankalin hukumomi kan matsalolin ilimi, lafiya da ci gaban al’umma.

A nasa jawabin, malami a Jami’ar Bayero da ke Kano, Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa, ya jaddada cewa dimokuraɗiyya ba za ta inganta ba tare da sa hannun jama’a ba, yana mai kira ga ’yan Najeriya da su ɗauki inganta shugabanci nagari a matsayin nauyin kowa.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka karrama, Dan Bello, ya ce kyautar ta ƙara masa ƙwarin gwiwar ci gaba da aikin jarida mai amfani ga jama’a, tare da taimaka wa matasa ’yan jarida su koyi wannan fanni.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments