Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeAmurka na shirin watsa yadda za a aiwatar da hukuncin kisa kan...

Amurka na shirin watsa yadda za a aiwatar da hukuncin kisa kan tsojon sojan ta kai tsaye

Gwamnatin Amurka ta sanar da shirin watsa yadda za a aiwatar da hukuncin kisa kan Nidal Malik Hasan, tsohon sojan Amurka da aka samu da laifin kashe sojoji 13 tare da raunata wasu 32 a sansanin sojojin Fort Hood da ke jihar Texas a shekarar 2009.

Rundunar sojojin Amurka ta bayyana cewa za a bindige Hasan a bainar jama’a, matakin da aka ce ba a aiwatar da irinsa cikin shekaru 65 ba, bayan kalaman Sakataren Yaƙi na Amurka, Pete Hegseth.

Hasan tsohon manjo ne a rundunar sojojin Amurka, kuma likitan ƙwaƙwalwa ne daga jihar Virginia.

A lokacin shari’arsa a shekarar 2013, ya amince da harbe sojojin, yana mai cewa ya aikata hakan ne domin kare Musulmai da mayakan Taliban daga hare-haren sojojin Amurka a Afghanistan.

An harbi Hasan yayin da yake kai harin, kuma tun daga lokacin yake amfani da kujerar guragu sakamakon raunin da ya samu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments