Wani bincike da jaridar PUNCH ta gudanar ya gano cewa masu ababen hawa a Najeriya sai sun sauke manhajar NNPCL ta wayar salula tare da biyan kuɗin mai ta intanet kafin su samu rangwamen ₦66 kan kowace litar man fetur.
Jaridar ta bayyana cewa a wasu gidajen man NNPC Retail da ke Abuja ranar Juma’a, ana sayar da litar man fetur a kan ₦1,405 ga kwastomomin da ke biyan kuɗi kai tsaye a famfo.
Sai dai masu amfani da manhajar NNPCL wajen biyan kuɗi suna samun rangwamen, inda suke sayen litar man a kan ₦1,339.
Wannan na nufin masu biyan kuɗi ta manhajar suna samun rangwamen ₦66 kan kowace lita idan aka kwatanta da waɗanda ke biyan kuɗi kai tsaye a gidan mai.
Binciken ya nuna cewa samun rangwamen na da alaƙa da amfani da manhajar da kuma biyan kuɗi ta intanet, maimakon biyan kuɗi kai tsaye a famfo.