Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin APC ta yi watsi da walwalar malamai a Najeriya – ADC...

Gwamnatin APC ta yi watsi da walwalar malamai a Najeriya – ADC PCC

Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar ADC (ADC-PCC) ya yaba wa malaman Najeriya bisa irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban ƙasa, tare da bayyana su a matsayin ginshiƙan da ke tsara makomar Najeriya.

Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar ADC (ADC-PCC) ya yaba wa malaman Najeriya bisa irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban ƙasa, tare da bayyana su a matsayin ginshiƙan da ke tsara makomar Najeriya.

A cikin saƙon taya murna da bikin Ranar Malamai ta Duniya ta 2026, Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na kwamitin, Kola Ologbondiyan, ya ce malamai sun ci gaba da koyar da yara da kuma gina halayensu duk da shekaru na rashin kulawa, wahalhalu da tabarbarewar yanayin aikin koyarwa.

Ologbondiyan ya bayyana malaman Najeriya a matsayin “jarumai”, inda ya yaba wa sadaukarwarsu, jajircewarsu da kishin ƙasa.

Ya ce: “Malaman Najeriya jarumai ne na gaskiya. Sun ci gaba da gina rayuwar yara, tarbiyyantar da su da kuma taimakawa wajen dorewar tsarin iliminmu duk da rashin kulawa da wahalhalu.“

“A wannan rana ta musamman, ADC-PCC na murnar sadaukarwa, jajircewa, juriyar aiki da kishin ƙasa da suke nunawa.”

Sai dai Ologbondiyan ya soki gwamnatin jam’iyyar APC kan abin da ya bayyana a matsayin ƙara tsanantar wahalhalun da malamai ke fuskanta.

Ya danganta matsalolin da cire tallafin man fetur ba tare da samar da isassun matakan rage wa jama’a radadi ba, ƙarancin albashi da rashin biyan sa a kan lokaci, ƙarancin kulawa da ma’aikata, rashin isasshen horo da sake horar da malamai, lalacewar gine-ginen makarantu da kuma tsadar rayuwa.

“Abin takaici ne yadda waɗanda ke koyar da yaranmu, waɗanda ke renon shugabannin gobe, likitoci, injiniyoyi da masana kimiyya, su kansu suke rayuwa cikin wahala,” in ji shi.

“Ta yaya malami zai koyar yadda ya kamata alhali yana fama da yunwa? Ta yaya malami zai bayar da iya ƙoƙarinsa idan ba zai iya samun kuɗin zuwa makaranta ba saboda tsadar man fetur, alhalin albashinsa bai isa biyan bukatunsa na wata ba, ba shi da isasshen inshorar lafiya kuma ba zai iya samun ingantaccen matsuguni ba?”

Ologbondiyan ya kuma zargi gwamnatin APC da rage darajar aikin koyarwa, yana cewa malamai da dama a makarantun firamare da sakandare na karɓar ƙaramin albashi, yayin da ma’aikatan manyan makarantun gaba da sakandare suka sha yin yajin aiki saboda matsalolin jin daɗi da yanayin aikinsu.

Duk da waɗannan ƙalubale, ya ce malamai sun ci gaba da gudanar da ayyukansu kuma sun cancanci ingantacciyar kulawa da kuma kyautata yanayin aikinsu.

Kakakin ADC-PCC ya ce gwamnatin ADC ƙarƙashin ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, za ta mayar da jin daɗin malamai da inganta fannin ilimi cikin manyan abubuwan da za ta ba fifiko idan aka zaɓe ta a 2027.

Ya ce jam’iyyar za ta mayar da hankali wajen biyan albashin da ya dace da tsadar rayuwa, inganta alawus-alawus, samar da cikakken inshorar lafiya, gidaje masu sauƙin samu, ci gaba da horar da malamai da kuma samar da kyakkyawan yanayin koyarwa da koyo.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments