Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiWaiya ya nemi limamai su wayar da kan jama’a kan illar bangar...

Waiya ya nemi limamai su wayar da kan jama’a kan illar bangar siyasa

Ƙungiyar Limaman Matasa na Masallatan Juma’a ta Arewa ta karrama Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Dr. Ibrahim Abdullahi Waiya, inda ta naɗa shi da muƙamin “Gwani”.

Ƙungiyar Limaman Matasa na Masallatan Juma’a ta Arewa ta karrama Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Dr. Ibrahim Abdullahi Waiya, inda ta naɗa shi da muƙamin “Gwani”.

An gudanar da bikin karramawar ne a wani taro na musamman da aka shirya domin bikin Khatamar Alƙur’ani, a zauren taro na Kwalejin Nazarin Addinin Musulunci da Shari’a ta Aminu Kano.

Da yake jawabi bayan karramawar, Kwamishina Waiya ya bayyana farin cikinsa tare da godiya ga limaman bisa wannan karamci, yana mai cewa karramawar ta ƙara masa nauyin da ke kansa na ci gaba da tallafa wa ayyuka da shirye-shiryen ƙungiyar.

Ya buƙaci limamai da malaman addini da su ƙara himma wajen wayar da kan al’umma, musamman matasa, kan illolin zagi da cin mutunci a siyasa, ɓata suna da daba, tare da amfani da matsayinsu wajen yaɗa zaman lafiya, haɗin kai da kishin ƙasa.

Kwamishinan ya ce limamai da malaman addini suna da matuƙar tasiri a cikin al’umma, saboda saƙonnin da suke isarwa suna isa ga dimbin jama’a, ciki har da shugabannin siyasa da na al’umma.

Ya kuma yi kira gare su da su yi amfani da mumbaransu wajen ƙarfafa w mutane su shiga harkokin siyasa cikin lumana, haƙuri da juriya, kyawawan ɗabi’u da tattaunawa mai amfani, musamman tsakanin matasa.

A nata ɓangaren, ƙungiyar ta bayyana godiyarta ga Kwamishina Waiya bisa irin goyon baya da ƙarfafa gwiwar da yake ba ta a ayyukanta daban-daban.

Limaman sun ce yadda Kwamishinan ke kasancewa a shirye wajen sauraron su da tallafa wa shirye-shiryensu ya zama abin ƙarfafa musu gwiwa, tare da nuna muhimmancin rawar da malaman addini ke takawa wajen samar da zaman lafiya da kyawawan ɗabi’u a cikin al’umma.

Ƙungiyar ta kuma yaba da kusancin Kwamishinan da malaman addini, tare da bayyana alaƙar da ke tsakaninsu a matsayin wadda ta ginu kan mutunta juna da haɗin gwiwa domin ci gaban al’umma.

A ƙarshe, Kwamishina Waiya ya tabbatar wa ƙungiyar cewa zai ci gaba da tallafa wa duk wani shiri mai amfani da take gudanarwa, yana mai jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da malaman addini wajen magance matsalolin da ke addabar al’umma da kuma inganta ci gaban Kano da Arewa baki ɗaya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments