Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki a faɗin Najeriya, domin girmama jami’an Rundunar Sojin Sama da suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin sama a Jihar Ondo.
Shugaban ya kuma bayar da umarnin sauke tutocin Najeriya zuwa ƙasa a duk faɗin ƙasar a matsayin alamar girmamawa da juyayin rasuwar jami’an.
Jirgin sojin ƙirar ATR-42 ya yi hatsari ne a kusa da sansanin Sojin Ruwa da ke yankin Igbokoda a Jihar Ondo, yayin da yake kan hanyarsa daga Benin da ke Jihar Edo zuwa Legas.
Rahotanni sun ce jirgin na ɗauke da fasinjoji 25 da kuma ma’aikatan jirgin bakwai a lokacin da hatsarin ya afku.
A cikin saƙon ta’aziyyarsa ga Babban Hafsan Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, da sauran jami’an rundunar, Tinubu ya bayyana hatsarin a matsayin babban rashi ga Rundunar Sojin Sama da Najeriya baki ɗaya.
Shugaban ya kuma umarci Rundunar Sojin Sama da ta gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin hatsarin, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin hana sake faruwar irin wannan lamari nan gaba.