Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya tabbatar da cewa mutane 32 ne ke cikin wani jirgin soji da ya yi hatsari a Igbokoda, Jihar Ondo.
Keyamo ya ce jirgin, mai lamba NGR 931, ya bace da misalin ƙarfe 9:13 na safe yayin da yake kan hanyarsa daga Benin zuwa Legas.
Ya ce jami’an kula da zirga-zirgar jiragen sama ne suka sanar da hukumomi bayan sun kasa samun damar tuntuɓar jirgin ta rediyo.
A cewar ministan, daga baya aka tabbatar da cewa jirgin sojin ya yi hatsari ne a kusa da sansanin sojin ruwa da ke Igbokoda, inda aka gano tarkacen jirgin.
Ya ce ana ci gaba da gudanar da ayyukan bincike da ceto domin gano wadanda ke cikin jirgin.
“Bayanan farko sun nuna cewa akwai fasinjoji 25 da kuma ma’aikatan jirgin guda bakwai a cikin jirgin,” in ji Keyamo.
Ministan ya bayyana cewa kula da jiragen soji da kuma sanya musu dokoki ba ya cikin hurumin Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya ko Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA).
Sai dai ya ce ya tattauna da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, tare da yin alkawarin cewa ma’aikatar za ta bayar da “cikakken hadin kai da taimako” wajen gudanar da ayyukan bincike da ceto.
“Za a fitar da karin bayani kan wannan mummunan lamari daga baya,” in ji shi.