An kama wani matashi mai suna Halifa Miko, bisa zargin caccakawa kishiyar mahaifiyarsa makami a wanda ya yi sanadin mutuwar ta har lahira a unguwar Dawanau da ke Kano.
Lamarin ya faru ne a safiyar Lahadi.
Mijin matar, mai suna Miko, ya bayyana damuwarsa kan lamarin, inda ya bukaci hukumomi da su ɗauki matakin da ya dace tare da hukunta wanda ake zargin bisa laifin da ake zargin ya aikata.
Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun kama wanda ake zargin tare da kai shi hedikwatar rundunar yan sanda dake Bompai, inda ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken abin da ya faru da kuma dalilin da ya haddasa lamarin.