Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasa'Duk ku ne': ADC ta kalubalanci Shettima kan gwamnatin Buhari

‘Duk ku ne’: ADC ta kalubalanci Shettima kan gwamnatin Buhari

Kwamitin ya ce APC ba za ta iya dora wa mulkin Buhari laifi yayin da take kare gwamnatin Tinubu ba

Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Ƙasa na ADCPCC ya soki ikirarin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ceci Najeriya daga durƙushewar tattalin arziki.

Kwamitin ya ce furucin Shettima cewa Najeriya na dab da shiga wani halin ni ‘yasu kafin Tinubu ya zama shugaban ƙasa, ya kuma nuna gazawar gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, wadda ita ma ta yi mulki ne a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ADCPCC, Kola Ologbondiyan, ya fitar ranar Lahadi, ya zargi Shettima da ƙoƙarin sauya tarihin APC yayin da yake kare abin da ya kira gazawar gwamnatin Tinubu.

Ologbondiyan ya ce idan da gaske Najeriya na fuskantar barazanar durƙushewar tattalin arziki kafin Tinubu ya karɓi mulki, to APC ya kamata ta ɗauki alhakin hakan, saboda ita ce ke jagorantar gwamnatin tarayya tsawon shekaru takwas a zamanin Buhari.

“Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ya yi magana ta tonawa kai asiri. Idan Najeriya na dab da shiga mawuyacin hali a ƙarƙashin Buhari, hakan na nufin Buhari da APC sun yaudari ’yan Najeriya tsawon shekaru takwas.”

“Idan haka ne, me ya sa ’yan Najeriya za su yarda da Tinubu, wanda yake daga cikin APC kuma ya kasance babban mai tallatawa da kare gwamnatin Buhari?” Ologbondiyan ya tambaya.

Ya ce APC ba za ta iya nisantar kanta da abubuwan da ta aikata a baya ba, yana mai tunatar da cewa Tinubu ya sha kare gwamnatin Buhari tare da yin alkawarin ci gaba da gina kan nasarorin gwamnatin.

A cewarsa, ƙoƙarin Tinubu da Shettima na ware gwamnatin yanzu daga gwamnatin Buhari na nufin sun amince cewa APC ta gaza wa ’yan Najeriya.

“Amma ’yan Najeriya ba su san Buhari a matsayin mutum ɗaya ba; ’yan Najeriya sun san APC. APC ce, wadda Shugaba Tinubu ke neman wa’adin mulki na biyu a ƙarƙashinta, ta gaza wa ’yan Najeriya kusan shekaru 12, kuma ba ta cancanci ƙarin shekaru huɗu ba,” in ji shi.

Ologbondiyan ya kuma zargi gwamnatin APC da gazawa a fannoni da dama.

“Hanyoyinmu sun daina zama masu sauƙin zirga-zirga, babu wutar lantarki, cibiyoyinmu sun durƙushe. Amma abin da ya fi damun talakawan Najeriya a yau shi ne abinci, abinci da abinci, ba farfaganda marar tushe ba.”

“Shugaba Tinubu bai ceci Najeriya daga durƙushewa ba; ya ƙara jefa ƙasar cikin matsanancin durƙushewar tattalin arziki, wanda yunwa da ba a taɓa ganin irinta ba, hauhawar farashi mai tsanani, faduwar darajar Naira, rashin tsaro, rashin aikin yi da tsadar rayuwa mai tsanani suka bayyana,” in ji shi.

Ya ƙaryata batun cewa Najeriya na dab da shiga yanayin “mawuyacin hali”, yana mai cewa tuni ’yan Najeriya ke rayuwa cikin irin wannan yanayi.

Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben ADC ya kuma nuna shakku kan alkawarin Shettima na samar da kekunan hawa masu amfani da lantarki 10,600, bas 300 da motocin haya masu amfani da lantarki a ƙarƙashin shirin e-logistics cikin makonni masu zuwa.

Ya tunatar da Mataimakin Shugaban Ƙasar cewa gwamnati ta taɓa yin alkawarin rage farashin sufuri zuwa ranar 1 ga Oktoba, 2026, yana mai cewa ya kamata ’yan Najeriya su auna gwamnati bisa abubuwan da ta aiwatar, ba sabbin alkawurra kawai ba.

Kwamitin ADCPCC ya yi kira ga Shettima da APC da su dakatar da abin da ya kira ƙoƙarin sauya tarihin siyasar ƙasar, maimakon haka su mayar da hankali kan matsalolin da ’yan Najeriya ke fuskanta.

Kwamitin ya ce ADC na nan daram wajen samar da wata madadin siyasa mai inganci da zai iya kawo ƙarshen mulkin APC, tare da yin kira ga ’yan Najeriya su mara wa gwamnatin da za ta sauƙaƙa rayuwa tare da dawo da daidaito da kwanciyar hankali a tattalin arziki baya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments