Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiYau Shekaru 30 Da Wafatin Shiekh Nasiru Kabara (RA).

Yau Shekaru 30 Da Wafatin Shiekh Nasiru Kabara (RA).

Shehi ya rasu a ranar 4 ga watan Oktoba 1996. Shehin ya rubuta littafan musulunci da dama akan Tafsiri da Hadisai, wadanda aka ce sun haura littafai sama da 300.

An haifi Nasiru Muhammad Al-Muktar Kabara a garin Guringawa dake cikin jihar Kano, a ranar 18 ga watan Afrilu 1912, an ce kakansa asalinsa ya fito ne daga tashar jiragen ruwa ta Kabara da ke kusa da kogin Neja a kasar Mali, bayan jihadin Usman Dan Fodio a (1804-8), daga nan ne ya yi hijira zuwa kasar Hausa, zuwa Masarautar Kano a karshen karni na sha takwas, inda ya sauka a fadar sarki, inda daga nan sarki ya ba shi fili ya zauna a unguwar Kabara da ke cikin birnin (wanda sunan unguwar ya samo asali daga garin Kabara na kasar Mali).

Shi ne wanda ya kafa Darul Qadiriyya (gidan Qadiriyya) a Jihar Kano, wanda mabiyan Qadiriyya a yammacin Afrika ke kallonta a matsayin cibiyar Qadiriyya ta yammacin Afrika. An ba shi lakabin Nasiru Kabara, Al-Sinhaji, Al-kadiri, Al-Maliki, Al-Ash’ari kuma sarkin yakin Usman Dan Fodio Shehu Usmanu Bin Fodiyo.

Ya Allah (SWT) Ya Kai Rahama Ga Malamin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments