Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNaira 70,000 ba zata taba wadatar da ma’aikatan Najeriya ba – Keyamo

Naira 70,000 ba zata taba wadatar da ma’aikatan Najeriya ba – Keyamo

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana cewa mafi ƙarancin albashin N70,000 da ake biyan ma’aikatan Najeriya a yanzu bai yi daidai da yanayin matsin tattalin arzikin da ake ciki ba.

Keyamo ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taron ƙasa na shekarar 2026 kan shirye-shiryen ma’aikata kafin ritaya, inda ya jaddada buƙatar sake duba mafi ƙarancin albashin domin rage wa ma’aikata nauyin matsin tattalin arziki.

Ministan ya ce gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago na buƙatar sake tattaunawa kan batun albashi tare da neman matsayar da za ta yi la’akari da halin tattalin arzikin ƙasar da kuma buƙatun ma’aikata.

Ya kuma bayyana cewa jin daɗin ma’aikata na da muhimmanci wajen samun ingantaccen aiki da ci gaba, saboda ma’aikata na taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da harkokin gwamnati da tattalin arzikin ƙasa.

Keyamo ya kuma tuna cewa yana cikin masu ruwa da tsaki da suka halarci tattaunawar da ta kai ga ƙarin mafi ƙarancin albashi daga N30,000 zuwa N70,000.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments