Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya sake bayyana ƙudirin gwamnatinsa na dawo da cikakken zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a faɗin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a taron Majalisar Zartarwar Jihar da aka gudanar ranar Alhamis, inda ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa wajen yaƙi da ayyukan ’yan bindiga ba har sai an tabbatar da tsaron al’umma.
Ya ce ɗaya daga cikin manyan manufofin gwamnatin tasa shi ne tabbatar da cewa mutanen da suka rasa matsugunansu sakamakon hare-haren ’yan bindiga sun samu damar komawa garuruwansu cikin aminci da mutunci.
Ahmad Aliyu ya bayyana cewa haɗin gwiwar gwamnatin jihar da hukumomin tsaro na haifar da sakamako, inda ya misalta ayyukan da aka gudanar a ƙananan hukumomin Rabah, Tureta da Kebbe, waɗanda suka taimaka wajen ceto wasu mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma kwato dubban dabbobin da aka sace.
Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro da kayan aikin da suke buƙata domin ƙara inganta ayyukan tabbatar da tsaro a jihar.
Ya kuma ce gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da ajandar ta mai kunshe da muhimman abubuwa tara, tare da ƙara mayar da hankali wajen samar da ci gaba mai ma’ana ga al’ummar jihar.