Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayar da tallafin Naira miliyan 20 ga iyalan mutane 37 da suka mutu a wani lamari da ya shafi jami’an Hukumar Tsaron Farar Hula ta Ƙasa (NSCDC) a Minna, Jihar Neja.
Atiku, wanda ke takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ya sanar da bayar da tallafin ne a ranar Talata, yayin ziyarar da ya kai ga iyalan waɗanda suka mutu da kuma mutanen da suka tsira daga lamarin.
A yayin ziyarar tasa, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma gana da Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago, da kuma tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya).
A cewar sanarwar da babban mataimakinsa na musamman kan hulɗa da jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya bayyana mutuwar matasan a matsayin babban abin takaici, wanda ke nuna irin ƙalubalen da matasan Najeriya ke fuskanta yayin ƙoƙarin neman abin dogaro da kai a cikin mawuyacin halin rayuwa.
Atiku ya ce Najeriya ba za ta iya tabbatar da kyakkyawar makomarta ba tare da zuba jari a matasa, faɗaɗa damar samun ayyukan yi da kuma ba su damar gudanar da sana’o’in halal masu amfani ba.
Ya kuma bayyana cewa abin da ya fi tayar masa da hankali shi ne bayanin da ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira ya yi masa, inda ya ce an cusa sama da mutane 68 a wani ƙaramin ɗaki yayin da ake tsare da su, kuma da dama daga cikinsu suka mutu.