Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da ƙarin kashi 95 cikin 100 kan albashin ma’aikatan lafiya a faɗin jihar.
Sabon tsarin albashin ya fara aiki daga ranar 7 ga Satumba 2026, kuma an tsara shi ne bisa tsarin albashin ma’aikatan lafiya da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi, musamman CONHESS.
Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin jihar, Shehu Baraya, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar 10 ga Satumba.
Gwamnatin ta ce ƙarin albashin na daga cikin matakan da gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ke ɗauka domin inganta harkar lafiya da jin daɗin ma’aikatan.
Ta kuma yi kira ga ma’aikatan da su mayar da martani ta hanyar ƙara himma, biyayya da bin dokokin aikin gwamnati domin inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar.