Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAtiku ya bukaci Tinubu ya fadi dalilinsa na 'kin halartar taron MDD...

Atiku ya bukaci Tinubu ya fadi dalilinsa na ‘kin halartar taron MDD shekaru 3 a jere

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa ‘yan Najeriya bayani kan dalilin da ya sa bai halarci babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) a shekarun 2024, 2025 da 2026 ba.

Atiku ya bayyana cewa, duk da cewa babu laifi a mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilci Najeriya a taron, maimaita hakan na iya hana Tinubu damar amfani da taron wajen ƙulla yarjejeniyoyin kasuwanci, jawo masu zuba jari da tattaunawa da shugabannin ƙasashen duniya.

A cewar rahoton Channels TV, Atiku ya kuma yi tambaya kan ko wasu batutuwan da suka shafi tarihin Tinubu da hukumomin Amurka na da alaƙa da rashin halartar taron, sai dai ya jaddada cewa bai ce an hana shugaban ƙasar shiga Amurka ba.

Ya buƙaci fadar shugaban ƙasa ta bayyana dalilin rashin halartar taron, matuƙar babu wani dalili na doka, diflomasiyya, lafiya ko na ƙashin kai da ya hana Tinubu zuwa taron karo na uku a jere.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments