Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su rage almubazzarancin abinci tare da rungumar hanyoyin tsaftace muhalli da kare lafiyar al’umma.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Oluremi ta yi wannan kiran ne a saƙon bikin Ranar Tsaftace Muhalli ta Duniya ta 2026, mai taken “Daga faranti masu tsabta zuwa birane masu tsabta.”
Ta jaddada muhimmancin rage zubar da abinci a gidaje da wuraren kasuwanci, zubar da shara a wuraren da suka dace da kuma haɗin gwiwar al’umma wajen tabbatar da tsaftataccen muhalli.
Oluremi ta ce haɗin kan al’umma wajen kare muhalli zai taimaka wajen samar da tsaftatattun wuraren zama da ingantacciyar lafiya ga al’umma ta yanzu da kuma al’ummomi masu zuwa.