Saturday, October 17, 2026
HomeTsaro’Yan Bindiga sun kashe mutane 13, tare da tilasta wa al’umma barin...

’Yan Bindiga sun kashe mutane 13, tare da tilasta wa al’umma barin gidajensu a Zamfara

Wasu ’yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 13 tare da tilasta wa mazauna wasu ƙauyuka uku barin gidajensu a yankin Masarautar Dansadau, ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.

Lamarin ya biyo bayan wani hari na ramuwar gayya, bayan da ’yan sa-kai suka kashe wani fitaccen shugaban ’yan bindiga tare da wasu daga cikin yaransa, inda suka kuma kwace bindigogin da suke amfani da su.

Wani mazaunin yankin ya ce ’yan bindigar sun zargi al’ummomin da hannu wajen taimaka wa ’yan sa-kai wajen kai farmakin.

Ya ce lamarin ya ƙara tsananta rikicin da ke tsakanin ’yan sa-kai da ’yan bindiga, inda ya ce ’yan bindigar sun hana al’ummar yankin yin noma tsawon kusan shekaru biyu.

Ƙauyukan da lamarin ya shafa sun haɗa da Dandallah, Tudu Gabas da Unguwar Majidadi.

Wani mazaunin yankin ya ce yawancin mazauna ƙauyukan, musamman mata da yara, sun tsere zuwa garin Dansadau domin neman mafaka, inda aka samar musu da abinci da matsuguni.

Wani mazaunin Dansadau ya ce ’yan bindigar na ci gaba da gudanar da ayyukansu a yankin ba tare da wata tangarda ba, tare da amfani da hanyoyin yankin wajen kai hare-hare ga mazauna Dansadau da sauran al’ummomin da ke kusa.

Rahoton ya ce an gano gawarwakin wasu daga cikin waɗanda aka kashe, yayin da rundunar ’yan sandan jihar Zamfara ta ce za ta binciki lamarin tare da bayar da ƙarin bayani.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments