Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMatasa kusan 40 sun rasu a hannun hukumar tsaro ta NSCDC

Matasa kusan 40 sun rasu a hannun hukumar tsaro ta NSCDC

An kama mutanen ne bisa zargin haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, yayin da aka dakatar da kwamandan NSCDC na jihar

Aƙalla mutane 37, ciki har da wasu matasa, sun mutu a hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) a Minna, babban birnin Jihar Neja.

An kama mutanen ne a ranakun 15 da 16 ga Satumba, 2026, bisa zargin yin haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda suka mutu ’yan gudun hijira ne daga wasu al’ummomi a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar.

Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, ya tabbatar da mutuwar mutane 37 a lamarin, inda ya ce an dakatar da Kwamandan NSCDC na jihar, Suberu Siyaka Aniviye.

Tun da farko, Aniviye ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda aka kama sun mutu ne a tsare bayan barkewar wata cuta da ake zargi a safiyar Alhamis.

Ya ce mutanen suna cikin waɗanda aka kama yayin wani samame da jami’an hukumar suka gudanar a Mohammed Inuwa Wushishi Housing Estate da ƙauyen Lukoto.

Sai dai kwamandan bai bayyana adadin waɗanda suka mutu ko irin cutar da ake zargin ta haddasa mutuwar ba.

A cikin wata sanarwa, Aniviye ya ce an gudanar da samamen ne domin dakile ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, inda aka kama mutane da dama tare da kwato wasu kayayyaki.

Ya ce a safiyar 17 ga Satumba an samu gawarwakin wasu daga cikin waɗanda ake tsare da su bayan zargin barkewar cuta.

An ce an kai gawarwakin zuwa Babban Asibitin Minna domin gudanar da bincike na likitanci da gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments