Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bayyana ra’ayinsa kan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, inda ya ce a ganinsa bai kamata ɗan takara daga Arewa ya kalubalanci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba a wannan zaɓen.
Shehu Sani ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya yi magana kan tsarin karɓa-karɓa tsakanin Arewa da Kudancin Najeriya da kuma yadda yake ganin ya kamata a tafiyar da shugabancin ƙasar.
A cewarsa, tun da shugabancin ƙasar yana hannun ɗan Kudu a halin yanzu, ya kamata ’yan takarar da za su fafata da Tinubu a 2027 su fito daga Kudancin Najeriya.
Ya ambaci Peter Obi, Omoyele Sowore, Seyi Makinde, Adewole Adebayo da Donald Duke cikin waɗanda yake ganin za su iya fafatawa.
Sanatan ya jaddada cewa tsarin karɓa-karɓa tsakanin Arewa da Kudu ba ya cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, amma yana ganin hakan wani salo ne na adalci da fahimtar juna tsakanin yankunan ƙasar.
Ya ce idan aka yi la’akari da wannan tsarin, Kudu ya kamata ta kammala wa’adin shekaru takwas na shugabanci kafin a bai wa Arewa damar neman mulki a 2031.
Sai dai, Shehu Sani bai fayyace yadda tsarin zai kasance idan ɗan Kudu ya sake lashe zaɓen 2027 ba, wanda hakan ka iya shafar batun karɓa-karɓa da ya yi magana a kai.