Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta ce ta ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su, tare da hallaka mutum uku da ake zargi da hannu a satar mutanen a yankin New Bussa.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, SP Wasiu Abiodun, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Minna, babban birnin jihar.
Abiodun ya ce an yi garkuwa da mutanen ne daga ƙauyen Wako a ranar 10 ga Satumba, inda masu garkuwar suka nemi a biya kuɗin fansa kafin a sako su.
Ya ce bayan samun bayanan satar, ’yan sanda tare da ’yan sa-kai sun shiga dajin Wawa domin gudanar da samame da ceto mutanen.
A cewarsa, jami’an tsaron sun yi musayar wuta da masu garkuwar yayin samamen, inda aka hallaka mutum uku da ake zargi da aikata laifin.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda ake zargin sun tsere daga wurin da raunukan harbi, yayin da jami’an tsaron suka samu nasarar kuɓutar da mutanen biyu ba tare da sun samu wani rauni ba.
Rundunar ta ce tana ci gaba da ƙoƙarin kamo sauran waɗanda ake zargin da suka tsere domin gurfanar da su a gaban doka.