Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanciBana fifita haihuwar ɗa namiji akan mace – Dangote

Bana fifita haihuwar ɗa namiji akan mace – Dangote

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce samun ɗa namiji da zai gaji daular kasuwancinsa ba shi ne fifikonsa ba.

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce samun ɗa namiji da zai gaji daular kasuwancinsa ba shi ne fifikonsa ba.

Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira da ARISE News, inda ya ce yana ganin ɗaya daga cikin ’ya’yansa mata uku na iya jagorantar kamfanin a nan gaba.

Ya ce ’ya’yansa mata, Halima, Fatima da Mariya, suna da ilimi da ƙwarewar da za su iya ɗaukar kamfanin zuwa wani mataki, yana mai cewa ba ya tilasta musu shiga harkar kasuwancin iyali.

Dangote ya ce ko da yake al’adun wasu wurare na fifita ɗa namiji a gadon dukiya, shi bai damu da hakan ba, domin a cewarsa, samun ɗa namiji ba ya tabbatar da nasarar kamfani ko ci gaban sunan iyali.

Ya ce babban burinsa shi ne gina tsarin gudanarwa da shugabanci na ƙwararru wanda zai tabbatar da dorewar Dangote Group, tare da barin tarihi na taimakawa wajen bunƙasa masana’antu a Afirka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments