Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP, Prince Adewole Adebayo, ya jajanta wa iyalan mutane tara da aka kashe a wani harin da ’yan bindiga suka kai kan fasinjojin bas a Jihar Plateau.
An kai harin ne a daren Lahadi a Dungus Junction da ke Kuru, ƙaramar hukumar Jos South, inda ’yan bindigar suka bude wuta kan fasinjojin.
Adebayo ya ce harin ya nuna gazawar gwamnati wajen cika babban nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata na kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.
Ya ce gwamnati na yawan yin Allah-wadai da hare-hare bayan sun faru, maimakon ɗaukar matakan da za su hana sake faruwar su. Ya kuma yi kira da a samar da tsarin tsaro mai ƙarfi wanda zai kare matafiya da sauran al’umma.
Adebayo ya yi alkawarin cewa idan aka zaɓe shi a 2027, zai mayar da tsaro cikin abubuwan da zai fi mayar da hankali a kansu a kwanaki 100 na farko, yana mai cewa waɗanda ke mulki a yanzu “suna barci a kan aiki.”