Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Sokoto ta rufe Masallacin Sheikh Musa Lukuwa

Gwamnatin Sokoto ta rufe Masallacin Sheikh Musa Lukuwa

Gwamnatin Jihar Sokoto ta bayar da umarnin rufe Masallacin Juma’a na Musa Lukuwa da ke Mabera, inda aka kai hari tare da kashe mutum, har sai an kammala bincike kan lamarin.

Gwamnatin ta kuma umarci hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin harin da kuma abubuwan da suka jawo rikicin da ya faru a masallacin.

A cikin wata sanarwa da Babban Daraktan Yaɗa Labarai na gwamnatin jihar, Abubakar Bawa, ya fitar, gwamnatin ta ce ta kafa wani kwamiti na musamman da ya ƙunshi malaman addini domin gudanar da bincike kan musabbabin rikicin addini da ya ɓarke a wasu sassan birnin Sokoto a kwanakin baya.

Kwamitin zai duba abubuwan da suka haddasa rikicin tare da gabatar da shawarwari ga gwamnatin jihar kan matakan da ya kamata a ɗauka domin tabbatar da zaman lafiya da kauce wa sake aukuwar irin wannan lamari.

Gwamnatin ta kuma jaddada cewa ba ta goyon bayan duk wani mutum, ko da kuwa yana da wani matsayi, da zai fake da sunan addini wajen cin mutunci ko raina Annabi Muhammad (SAW), iyalansa, ko sahabbansa.

Ta ce za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kare zaman lafiya da haɗin kan al’ummar jihar, tare da tabbatar da cewa ana bin doka wajen magance duk wani rikici da ya shafi addini.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments