Jam’iyyar ADC ta gargadi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) kan amfani da malaman jami’a da suka bayyana goyon bayansu ga ’yan siyasa a matsayin jami’an tattara da haɗa sakamakon zaɓen 2027.
Kiran na ADC ya biyo bayan rahoton cewa sama da manyan malaman jami’o’in gwamnati 600 a Arewa sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Jam’iyyar ta ce amfani da malaman da suka fito fili suka bayyana goyon bayansu ga wani ɗan takara wajen tattara ko bayyana sakamakon zaɓe na iya haifar da tambayoyi kan sahihancin zaɓen tare da tayar da batun rikicin muradun juna.
Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce malaman jami’a suna da ’yancin tallafa wa ɗan takarar da suke so, amma bai kamata a naɗa wanda ya bayyana irin wannan goyon baya a matsayin jami’in da zai shiga aikin tattara ko bayyana sakamakon zaɓen da ɗan takarar ke fafatawa ba.
A cewarsa, ya kamata INEC ta samar da ƙa’idojin da za su hana mutanen da suka fito fili sun goyi bayan ’yan takara ko suka shiga harkokin siyasa masu alaƙa da jam’iyyu zama jami’an tattara da haɗa sakamakon zaɓe.
ADC ta kuma bukaci INEC ta wallafa sunayen jami’an da za su gudanar da aikin tattara da haɗa sakamakon zaɓe tun kafin ranar zaɓe.
Jam’iyyar ta ce hakan zai bai wa jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki damar duba sunayen jami’an tare da nuna duk wani abin da za su iya ɗauka a matsayin rikicin muradun juna kafin gudanar da zaɓen.