Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce hare-haren Boko Haram sun lalata gine-ginen makarantu sama da 5,000, tare da barin yara miliyan 2.2 ba sa zuwa makaranta a lokacin da rikicin ya yi kamari.
Zulum ya bayyana hakan ne a Maiduguri ranar Lahadi, yayin ƙaddamar da wasu ayyukan raya jihar da Gwamnan Nasarawa, Abdullahi A. Sule, ya yi. Ya ce rikicin ya kuma yi sanadin mutuwar malamai da masu gudanar da makarantu da dama.
Gwamnan ya ce gyaran makarantu ba wai gina gine-gine kawai ba ne, illa dawo da damar samun ilimi da kuma sake gina amincewar al’umma. Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kashe sama da N46.9 biliyan kan ilimin firamare da sakandare a shekarun kasafin kuɗi na 2025 da 2026.
Zulum ya ce a yanzu adadin azuzuwan da ake amfani da su a jihar ya karu zuwa 5,792, yayin da cibiyoyin tsafta da ruwan sha na makarantu suka kai 4,563. Haka kuma, makarantu masu aiki na sakandare sun karu daga 34 a ƙananan hukumomi takwas a 2019 zuwa 129 a ƙananan hukumomi 25 a 2026.
Ya ce wannan ƙarin damar samun ilimi ya sa yawan ɗaliban da ke makarantu ya tashi daga 766,551 a 2019 zuwa 1,801,295 a 2026, wanda ke nuna ƙarin sama da ɗalibai miliyan ɗaya cikin shekaru bakwai.