Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane da AK-47...

An kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane da AK-47 a Edo

Sojojin Brigade ta 4 ta rundunar sojin Najeriya sun kama wani mutum da ake zargin mai garkuwa da mutane ne, Olamide Oyeniyi, tare da kwato bindigar AK-47 da alburusai a Jihar Edo.

Sojojin Brigade ta 4 ta rundunar sojin Najeriya sun kama wani mutum da ake zargin mai garkuwa da mutane ne, Olamide Oyeniyi, tare da kwato bindigar AK-47 da alburusai a Jihar Edo.

An kama wanda ake zargin ne yayin wani samame na musamman da sojojin suka gudanar a ranar 12 ga Satumba 2026, a Obaretin Community da ke kan hanyar Benin zuwa Sapele, a ƙaramar hukumar Ikpoba-Okha.

Kakakin rundunar, Kyaftin Kennedy Anyanwu, ya ce sojojin na gudanar da aikin ne domin dakile ayyukan masu aikata laifuka da kuma kare manyan hanyoyin sufuri a yankin.

Ya ce daga cikin abubuwan da aka kwato akwai bindigar AK-47 guda ɗaya, kwanson harsashi guda ɗaya da kuma harsasai takwas, baya ga wayar Tecno, jakunkuna biyu, tocila, akwatin kiɗa da tsafe-tsafe.

An ce wanda ake zargin yana hannun jami’an tsaro domin ci gaba da bincike, yayin da ake ƙoƙarin gano alakar sa da sauran masu aikata laifuka da kuma tantance ko yana da hannu a ayyukan garkuwa da mutane da sauran laifuka a yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments