Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiPDP ta zargi gwamnan Gombe da yin sakaci kan yaɗuwar cutar diphtheria

PDP ta zargi gwamnan Gombe da yin sakaci kan yaɗuwar cutar diphtheria

Jam’iyyar PDP reshen Jihar Gombe ta zargi gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da rashin ɗaukar matakan da suka dace kan rahotannin ɓullar cutar mashako, wato diphtheria, a wasu sassan jihar.

A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na PDP a jihar, Abdulkadir Ahmad Dukku, ya fitar ranar Lahadi, jam’iyyar ta ce rahotannin ɓullar cutar a wasu jihohin Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya na buƙatar gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa domin kare lafiyar jama’a.

PDP ta bayyana diphtheria a matsayin cuta mai haɗari wadda ke iya shafar maƙogwaro da hanyoyin numfashi, musamman ga yara, tana mai kira ga gwamnati da ta ƙarfafa wayar da kan jama’a da matakan kariya.

Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa wasu mutane da ake kyautata zaton suna ɗauke da cutar an kwantar da su a Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya da ke Gombe, yayin da aka samu wasu rahotanni daga cibiyoyin lafiya da ke Kumo, Bajoga da Billiri.

A cewar PDP, ya kamata gwamnatin jihar ta fito fili ta sanar da jama’a ainihin halin da cutar take ciki, tare da ɗaukar matakan gaggawa a makarantu da sauran wuraren da jama’a ke taruwa.

Jam’iyyar ta kuma yi kira da a samar da riga-kafi da magunguna, tare da ƙara wayar da kan jama’a domin hana cutar yaɗuwa zuwa wasu sassan jihar.

PDP ta ce lafiyar al’ummar Gombe ya kamata ta kasance cikin abubuwan da gwamnatin jihar ta fi bai wa muhimmanci, tana mai neman gwamnatin ta bayyana matakan da take ɗauka domin dakile cutar.

Sai dai zarge-zargen PDP na zuwa ne a matsayin matsayar jam’iyyar adawa, yayin da ake buƙatar martanin gwamnatin jihar domin jin matsayinta kan batun.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments