Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ranar 9 ga Satumba 2026 a matsayin ranar fara yaƙin neman zaɓen kujerun gwamna da na Majalisun Dokokin Jihohi a zaɓen 2027.
Matakin ya biyo bayan fara kamfen ɗin neman kujerar shugaban ƙasa da na Majalisar Dokokin Tarayya, wanda aka fara ranar 19 ga Agusta 2026.
Fara kamfen ɗin zai bai wa ’yan takarar gwamna da masu neman kujerun Majalisun Dokokin Jihohi damar gabatar da manufofinsu ga masu zaɓe ta hanyar tarukan jama’a, kafafen yaɗa labarai, tattaunawa da sauran hanyoyin da doka ta amince da su.
A jadawalin INEC, za a gudanar da zaɓen gwamna da na Majalisun Dokokin Jihohi a ranar 6 ga Fabrairu 2027.
Yayin da kamfen ɗin ya fara, ana sa ran fafatawar siyasa za ta ƙara ɗaukar zafi a jihohin da za a gudanar da zaɓen, yayin da ’yan takara da jam’iyyunsu za su fara neman goyon bayan masu kaɗa ƙuri’a.