Wata mata da ake zargi da kasancewa mamba a wata ƙungiyar safarar yara, Adejoke Popoola, ta amsa cewa ta sayar da wasu daga cikin ’ya’yan da ta haifa, tare da sace wasu yara 19 domin sayar da su.
Popoola ta bayyana hakan ne yayin da take magana da manema labarai a hedikwatar rundunar ’yan sandan Jihar Oyo da ke Ibadan, inda ta ce ta fara aikata laifukan tun watan Oktoban 2024.
Ta ce ta sayar da jariri namiji da kuma tagwaye, inda ta bayyana cewa ta sayar da tagwayen ga wani asibiti a Ogeere kan kuɗi N300,000.
A cewarta, tana sayar da yara ne idan mutumin da ya yi mata ciki ya ƙi ɗaukar nauyin cikin.
Ta ce a wasu lokuta tana karɓar tsakanin N80,000 zuwa N120,000 kan kowane yaro da ta sayar.
Popoola ta kuma bayyana cewa tana da ’ya’ya bakwai, wasu daga cikinsu sun yi aure, inda ƙaramin ɗanta ke da shekara shida, yayin da babbanta ke da shekara 34.
Bayan haka, ta amsa cewa tana satar yara, inda ta kan yi kamar tana neman gidan haya. Idan ta samu damar ganin yara ba tare da iyayensu ba, sai ta sace su.
Ta ce wata mata da ta yi aiki tare da ita a kasuwar Ogeere ce ta koya mata yadda ake satar yara.
Haka kuma, Popoola ta ce a wasu lokuta tana yin kamar ’yar bokanci ko mai maganin gargajiya, inda take yaudarar iyayen da ke da yara masu nakasa da alkawarin warkar da su, kafin ta sace wani yaro ta ba su.
Ta kuma bayyana cewa tana haɗa wannan sana’a da sayar da magungunan gargajiya a Ariyo Bus Stop, Olunloyo.
Popoola ta ba da labarin yadda ta ce ta sace wani yaro ɗan shekara uku mai suna Ifakunle Ifagbenro yayin bikin Egungun a garin Oyo.
A cewarta, daga cikin yara 19 da ake zarginta da sacewa, shida sun mutu, yayin da 13 ke raye.
Tun da farko, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta bayyana cewa ta bankado wata ƙungiyar satar yara da safarar su da ke gudanar da ayyukanta a tsakanin jihohi.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Abimbola Olugbenga, ya ce rundunar ta ceto yara 17 tare da kama mutum bakwai da ake zargi da hannu a lamarin.
Ya ce binciken da ya fara biyo bayan samun wata ƙorafi ya kai ga gano wata babbar hanyar aikata laifuka da ake zargin tana da hannu wajen satar yara, safarar su, sayar da su da kuma ɓoye su.