Lauyan wata ‘yar kasar Morocco, Khadija Diab, Bilkisu Abdulrasheed Chedi, ta ce Khadija ba ta tare da malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, kamar yadda mijinta, Nasiru Idris Musa, ya yi ikirari a shafukan sada zumunta.
Chedi ta bayyana cewa Khadija tana kasar Morocco tun watan Afrilu na 2026.
Daraktar zartarwa ta kungiyar Women Aware of Rights Initiative, ta ce Khadija ta koma Morocco a watan Afrilu bayan kungiyar ta taimaka mata wajen samun takardar tafiye-tafiye ta gaggawa, sakamakon zargin cewa mijinta ya karbe mata fasfo din kasa da kasa.
Ta bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ta wallafa, inda ta yi bayani kan yadda lamarin ya faru.
An yada faifan bidiyon ne a shafin Facebook da aka tabbatar na Dr Ahmad Gumi a ranar Talata, a daidai lokacin da ce-ce-ku-ce ke ci gaba bayan kalaman mijin Khadija a kafafen sada zumunta.
A cewar lauyan, Khadija ta shafe kusan watanni shida a Morocco, kuma a halin yanzu tana tare da iyalanta.
Ta ce: “Saboda haka, duk zarge-zargen cewa tana tare da Sheikh Gumi karya ne kuma ba su da tushe, domin ba zai yiwu mutum ya kasance a kasashe biyu daban a lokaci guda ba.”
Chedi ta ce bayan Khadija ta isa Morocco, iyalanta sun tuntubi kungiyar inda suka tabbatar mata cewa ta isa lafiya kuma tana zaune tare da su.
Ta ce Khadija ta tuntubi kungiyar Women Aware of Rights Initiative a watan Oktoban 2025, inda ta zargi mijinta da cin zarafinta a gida, rashin isasshen abinci da kulawa, da kuma tilasta mata abin da ta bayyana a matsayin “alakar aure da ba ta dace da doka ba kuma ba ta dabi’a ba.”
A cewar lauyan, kungiyar ta shawarci Khadija da ta gudanar da gwaje-gwajen lafiya bisa zarge-zargen da ta gabatar, inda sakamakon ya nuna cewa ta kamu da cututtukan da ake dauka ta hanyar jima’i.
Ta ce daga bisani Khadija ta bayyana karara cewa ba ta son ci gaba da zaman aure, tana zargin mijinta da cin zarafinta ta fuskar tunani da kuma jiki.
Chedi ta ce an shigar da kara a madadin Khadija a Kotun Shari’ar Musulunci ta Area da ke Daura Road, Kaduna, inda aka fara sauraron karar a ranar 3 ga Oktoban 2025.
Ta ce daga bisani aka dage karar zuwa ranar 11 ga Nuwamban 2025, bayan lauyan wanda ake kara ya shigar da bukatar sulhu.
A cewarta, an samu tsaiko a shari’ar bayan wanda ake kara ya sauya lauyansa, inda sabon lauyan ya kalubalanci hurumin kotun.
Ta kara da cewa rashin halartar lauyoyi a zaman kotun da kuma yajin aikin alkalai a Kaduna sun kara jinkirta shari’ar, abin da ya sa Khadija ta shiga damuwa ta fuskar tunani tare da nuna sha’awar komawa gida.
Chedi ta ce saboda zargin cewa mijin Khadija ne ke rike da fasfon ta na kasa da kasa, kungiyar ta taimaka mata wajen samun takardar tafiye-tafiye daga Masarautar Morocco.
Ta ce jami’an shige da fice na Morocco sun tabbatar da cewa Khadija ta isa kasar lafiya, yayin da Ofishin Jakadancin Morocco da ke Najeriya ma ya sanar da kungiyar cewa ta isa.
Lauyan ta ce kafin Khadija ta bar Najeriya, ta ba ta izinin ci gaba da shari’ar a madadinta.
Ta ce an dakatar da karar da ake yi a Kotun Shari’ar Daura Road a ranar 10 ga Yunin 2026, yayin da aka sake shigar da wata kara a watan Yulin 2026 domin neman raba auren bisa dokar Shari’a.
Chedi ta bukaci jama’a da su yi watsi da ikirarin cewa ana tsare da Khadija a hannun Sheikh Gumi, tana mai cewa manufar bayanin nata ita ce “warware rudanin” da ya taso kan inda Khadija take.