Ana sa ran fitattun taurarin ƙwallon ƙafa, Lionel Messi da Cristiano Ronaldo, su haɗu a ƙungiya ɗaya a wasan bankwanan tsohon ɗan wasan Manchester United da Manchester City, Carlos Tévez.
Tévez ya bayyana cewa yana da burin ganin manyan taurarin biyu sun taka leda tare a gefe guda domin bai wa masoya ƙwallon ƙafa damar shaida wani tarihi na musamman.
Za a gudanar da wasan bankwanan ne a filin La Bombonera da ke Buenos Aires a watan Disamban 2026.
A cewar Tévez, ya tuntubi Cristiano Ronaldo domin neman ya halarci wasan tare da Messi, kuma duka ’yan wasan sun nuna amincewarsu da shirin.
Idan har hakan ta tabbata, masoya ƙwallon ƙafa za su shaida Messi da Ronaldo suna taka leda a ƙungiya ɗaya a karo na musamman.