Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya nemi Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), da ya biya shi Naira biliyan 10 a matsayin diyya, tare da neman afuwar jama’a kan kalaman da ya yi a kansa.
Lauyoyin El-Rufai ne suka gabatar da wannan buƙata a cikin wata wasiƙar gargadin ɗaukar matakin shari’a da suka aikawa Ministan Tsaron.
Rahotanni sun ce an bai wa Janar Christopher Musa wa’adin kwanaki bakwai ya janye kalaman da ake zargi ya yi kan El-Rufai, ya nemi afuwa tare da biyan Naira biliyan 10 a matsayin diyya.
Lauyoyin tsohon gwamnan sun bayyana cewa kuɗin ba hukuncin kotu ba ne, illa buƙatar diyya kafin a ɗauki matakin shari’a.
Takaddamar ta samo asali ne bayan kalaman da Christopher Musa ya yi kan zargin cewa El-Rufai ya kitsa kashe-kashe a Kudancin Kaduna, zargin da tsohon gwamnan da iyalansa suka musanta tare da buƙatar a gabatar da hujjoji ko a janye kalaman.