Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiKano: Al’ummar Kankarofi sun koka kan rashin wutar lantarki na makonni 2

Kano: Al’ummar Kankarofi sun koka kan rashin wutar lantarki na makonni 2

Mazauna unguwar sun shafe sama da kwanaki 14 ba tare da wutar lantarki ba.

Al’ummar unguwar Kankarofi da ke birnin Kano sun koka kan rashin wutar lantarki da suka ce ya shafe sama da kwanaki 14.

Mazauna unguwar sun ce matsalar ta jefa su cikin mawuyacin hali, musamman saboda har yanzu ba su san abin da ya haddasa katsewar wutar ba.

Sun kuma ce kamfanin rarraba wutar lantarki na KEDCO bai bayyana musu dalilin matsalar ko lokacin da ake sa ran za a dawo da wutar ba.

Wani mazaunin unguwar ya shaida wa ICONIC TIMES cewa sun yi kokarin tuntubar lambar da aka ba su domin kai rahoton matsalar, amma ba su samu nasarar shiga layin ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments