Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaKuskure ne Peter Obi ya zaɓi Kwankwaso a matsayin mataimaki – NNPP

Kuskure ne Peter Obi ya zaɓi Kwankwaso a matsayin mataimaki – NNPP

Jam’iyyar NNPP ta ce jam’iyyar NDC ta yi babban kuskure wajen zaɓar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Peter Obi a zaɓen 2027.

Sakataren jam’iyyar NNPP na ƙasa, Ogini Olaposi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya yi suka mai ƙarfi kan matakin da jam’iyyar NDC da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, suka ɗauka.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito Olaposi na cewa, a ra’ayinsu, zaɓen Kwankwaso a matsayin abokin takarar Peter Obi na iya jefa jam’iyyar NDC cikin matsala a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa matakin na iya haifar da ƙalubale ga jam’iyyar NDC wajen neman gagarumin goyon bayan masu zaɓe a sassan ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments