Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiShugaban AU ya yi Allah-wadai da yunƙurin juyin mulki a Nijar

Shugaban AU ya yi Allah-wadai da yunƙurin juyin mulki a Nijar

Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka (AU), Mahmoud Ali Youssouf, ya yi Allah-wadai da yunƙurin boren sojoji da aka dakile a Yamai, babban birnin Nijar.

A ranar Asabar ne Ma’aikatar Tsaron Nijar ta sanar da cewa dakarun gwamnati sun dakile yunƙurin boren da wasu sojoji suka yi a cikin rundunar ƙasar.

A cikin wata sanarwa da AU ta fitar, Youssouf ya bayyana damuwarsa kan tashe-tashen hankulan, tare da yin tir da duk wani yunƙuri na kwace mulki ta hanyar amfani da ƙarfi.

Shugaban AU ya yi kira ga dukkan waɗanda ke da hannu a lamarin da su yi taka-tsantsan, tare da kare tsaro, zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’ummar Nijar.

Rahotannin kafofin watsa labarai sun ce rikicin ya yi sanadin mutuwar mutane biyar, ciki har da wasu dakarun da ke yaƙi da gwamnatin ƙasar.

AU ta kuma sake jaddada matsayinta na neman a dawo da tsarin mulkin dimokuraɗiyya da na kundin tsarin mulki a Nijar.

A halin yanzu, Janar Abdourahamane Tiani, shugaban gwamnatin sojin Nijar, bai yi wani jawabi kai tsaye kan lamarin ba. Sai dai ofishinsa ya ce ya tattauna ta wayar tarho da Shugaban Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune, yayin da Aljeriya ta tura jiragen yaƙi zuwa Yamai bisa buƙatar Nijar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments