Iyalan fitaccen mawakin Amurka, Tupac Shakur, sun bayyana farin ciki da sauƙin zuciya bayan samun hukunci a shari’ar da ta shafe shekaru ana binciken mutuwarsa.
Aiysha Obafemi, ‘yar uwa ga Tupac da ta halarci zaman shari’ar, ta ce iyalan sun ji daɗin hukuncin tare da nuna godiya ga duk waɗanda suka taimaka wajen ganin an gano gaskiyar lamarin.
Ta kuma karrama mahaifiyar Tupac, Afeni Shakur, wadda ta shafe tsawon lokaci tana fafutukar ganin an gano gaskiyar abin da ya faru da ɗanta.
Shari’ar ta shafi mutuwar Tupac, wanda aka harbe a Las Vegas a shekarar 1996 yana da shekara 25. Lamarin ya kasance cikin manyan kisan gilla da aka shafe shekaru ana neman wanda ke da alhaki.
Iyalan sun ce hukuncin ya kawo musu wani sabon salo na kwanciyar hankali, bayan kusan shekaru 30 suna jiran a samu adalci kan mutuwar mawakin.