Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaWasu jagororin siyasar Gawuna na shirin ficewa daga NDC zuwa APC

Wasu jagororin siyasar Gawuna na shirin ficewa daga NDC zuwa APC

Wasu daga cikin jagororin siyasar tsohon mataimakin gwamnan Kano kuma ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, Nasiru Yusuf Gawuna, sun gana da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, domin tattaunawa kan yiwuwar ficewarsu daga jam’iyyar NDC zuwa APC.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Siyasarmu TV cewa mahalarta taron sun gabatar wa Gwamna Abba Kabir Yusuf buƙatarsu, inda ta ce gwamnan ya amince da matakin.

A cewar majiyar, yanzu jagororin za su koma wurin magoya bayansu domin sanar da su matakin da suka ɗauka, kafin su bayyana a hukumance ficewarsu daga NDC zuwa APC.

Daga cikin waɗanda aka ce sun halarci ganawar akwai Hon. Badaru Ungogo, Mansur Gawuna, Ali Datti Yako, Comrade Abdurrahman Jibga, Umar Faruq BBD, Sani Dan Zara, Uba Ɗan Zainab, Sani Indabo, Sale Akwashe, Hassan Abba Abdullahi da Kabiru Bala.

Rahoton ya ce matakin ya biyo bayan rashin jituwar da ake zargin ta samu tsakaninsu da Nasiru Yusuf Gawuna. A cewar rahoton, bayan wasu daga cikinsu sun fice daga APC a baya, sun koma ADC, daga bisani kuma suka bi Rabiu Musa Kwankwaso zuwa NDC.

Rahoton ya ƙara da cewa wasu daga cikinsu sun kasance masu neman takara a matakai daban-daban, ciki har da Majalisar Tarayya, Majalisar Jiha da kujerar Sanata, amma ba a ba su damar samun kujerun takara ba, sai dai kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya da aka bai wa Nasiru Yusuf Gawuna.

Haka kuma, majiyar ta yi zargin cewa wasu daga cikin jagororin ba su gamsu da yadda aka tafiyar da harkokin siyasar ba, lamarin da ya sa suka fara neman wata mafita ta siyasa.

A halin yanzu, ana jiran sanarwar waɗannan jagororin a hukumance domin tabbatar da ko za su fice daga NDC su koma APC.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments