Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiMajalisa ta dakatar da kansiloli biyu kan zargin taba mutuncin Gwamnatin Kano

Majalisa ta dakatar da kansiloli biyu kan zargin taba mutuncin Gwamnatin Kano

Majalisar Kansilolin Ƙaramar Hukumar Tarauni a Jihar Kano ta dakatar da kansiloli biyu na tsawon watanni uku bisa zargin aikata wasu laifuka da suka haɗa da kalaman da aka bayyana a matsayin cin zarafi da taɓa mutuncin Gwamnan Kano, mataimakinsa da kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Tarauni.

A wata takardar dakatarwa da Siyasarmu TV ta gani, mai lamba TRLG/LC/31-08-2026/05, wadda aka fitar a ranar 31 ga Agusta, 2026, majalisar ta ce ta karɓi wasu korafe-korafe daga jama’a kan kansilolin mazabun Babbangiji da Unguwar Uku Cikin Gari.

Kansilolin da matakin ya shafa su ne Hon. Mukhtar Sani Ya’u, kansilan mazabar Babbangiji, da Hon. Kabiru Sabo Shu’aibu, kansilan mazabar Unguwar Uku Cikin Gari.

Majalisar ta ce korafe-korafen sun shafi wasu kalamai da ayyukan kansilolin da ta bayyana a matsayin cin zarafi da kuma taɓa mutuncin shugabannin gwamnati da na ƙaramar hukumar.

Bayan gudanar da doguwar muhawara kan batun, majalisar ta bayyana cewa ta gamsu da korafe-korafen da aka gabatar mata, sannan ta amince da dakatar da kansilolin biyu na tsawon watanni uku.

Matakin ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar Kansilolin Ƙaramar Hukumar Tarauni, Hon. Ali Idris Ali.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments