’Yan bindiga sun kashe mutane huɗu tare da yin garkuwa da wasu huɗu a ƙauyen Gorau, Ƙaramar Hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na daren Laraba, kwanaki shida kacal bayan hatsarin kwale-kwale da ya yi sanadin mutuwar mutane 65 a yankin.
Maharan sun kuma harbi mutane 11, inda huɗu suka mutu nan take, yayin da sauran bakwai ke karɓar magani a asibiti.
An ce ’yan bindigar sun kai harin ne domin neman kuɗin tallafin Naira miliyan ɗaya da gwamnatin Sokoto ta ware wa kowane iyalan waɗanda suka rasa ’yan uwansu a hatsarin.
Shugaban ƙauyen Gorau, Alhaji Aliyu Magaji Na-Batsami, ya ce maharan sun shiga gidaje suna tambayar inda aka ajiye kuɗin, amma jami’an tsaro sun isa wurin cikin gaggawa tare da fatattakar su.