Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanciMotar sojoji ta murƙushe ’yan kasuwa 5 a Taraba

Motar sojoji ta murƙushe ’yan kasuwa 5 a Taraba

Akalla ’yan kasuwa biyar ne suka mutu bayan wata motar sojoji kirar Hilux ta kwace ta kutsa cikin wata kasuwa a garin Chanchangi, Ƙaramar Hukumar Takum ta Jihar Taraba.

Akalla ’yan kasuwa biyar ne suka mutu bayan wata motar sojoji kirar Hilux ta kwace ta kutsa cikin wata kasuwa a garin Chanchangi, Ƙaramar Hukumar Takum ta Jihar Taraba.

Lamarin ya faru ne ranar Laraba yayin da motar ke rakiyar wasu ’yan kasuwa daga Wukari zuwa Takum, saboda yawaitar sace-sacen mutane a kan hanyar.

Wani mazaunin yankin, Tony David, ya ce wadanda suka mutu na daga cikin ’yan kasuwar da ke sayar da hajarsu a gefen hanya. Ya ce wasu ’yan kasuwa da dama sun samu raunuka.

An kai gawawwakin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Gwamnati na Takum domin kula da wadanda suka samu raunuka.

Kakakin ’yan sandan Taraba, ASP Victor Mshelizah, ya ce bai samu cikakken bayani kan lamarin ba, sai dai ya ce zai tuntubi jami’in ’yan sanda na Takum domin tabbatar da adadin wadanda suka mutu da sauran bayanai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments