Kungiyar Atlético Madrid ta bayyana cewa ba za ta tattauna da Barcelona kan yiwuwar sayar da ɗan wasanta, Julián Alvarez ba.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, kwamitin gudanarwar Atlético Madrid ya ce ya amince baki ɗaya da matakin ƙungiyar na kin tattaunawa da Barcelona kan Alvarez.
Atlético ta ce a shirye take ta tattauna cinikayyar ’yan wasa cikin mutunci da ƙwarewa, amma ta zargi Barcelona da rashin cika waɗannan sharuɗɗan, saboda haka ba a yi wata tattaunawa ba, kuma ba za a yi ba.
Ƙungiyar ta kuma ce tana da yakinin Alvarez zai fahimci matakin da aka ɗauka, sannan ya ci gaba da mai da hankali wajen taimaka wa Atlético cimma manufofinta.
Alvarez ya koma Atlético Madrid ne a shekarar 2024, kuma ya ci gaba da kasancewa cikin manyan ’yan wasan ƙungiyar tun bayan komawarsa daga Manchester City.