Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeYariman Saudiyya Mohammed bin Salman zai kai ziyarar aiki Faransa

Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman zai kai ziyarar aiki Faransa

Yariman Saudiyya kuma Firaministan ƙasar, Mohammed bin Salman, zai kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Faransa, inda Shugaban ƙasar, Emmanuel Macron, zai karɓe shi a birnin Paris.

A cewar rahotanni, ziyarar za ta mayar da hankali ne kan ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da haɗin gwiwa tsakanin Faransa da Saudiyya.

Ana kuma sa ran shugabannin biyu za su tattauna muhimman batutuwan tsaro, da kuma halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ƙasashen biyu ke ƙara ƙarfafa haɗin gwiwarsu kan batutuwan siyasa, tattalin arziki da tsaro a matakin ƙasa da ƙasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments