Gwamnatin Tarayya ta ce duk wani yunkuri na dawo da tallafin man fetur zai iya mayar da Najeriya cikin matsalolin tattalin arziki da ta fara fita daga cikinsu bayan cire tallafin.
Ministan Kudi kuma Ministan da ke kula da harkokin tattalin arziki, Dr. Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa cire tallafin ya samar da karin kudaden da suka bai wa Gwamnatin Tarayya, jihohi da kananan hukumomi damar aiwatar da muhimman ayyuka.
A cewar bayanan da aka gabatar a cikin kundin “Nigeria’s Reform Scorecard: The Benefits, Costs and Harms Prevented,” an samu kusan naira tiriliyan 15.8 a matsayin karin albarkatun da aka samu daga ajiyar da aka yi sakamakon cire tallafin tsakanin Yuni 2023 da Disamba 2025.
Rahoton ya ce daga cikin kudaden, kusan naira tiriliyan 5.43 sun samu ga Gwamnatin Tarayya, yayin da jihohi suka samu naira tiriliyan 6.52, sannan kananan hukumomi suka samu kusan naira tiriliyan 3.88.
Gwamnatin ta bayyana cewa wadannan kudade ba wai suna zaune ne a wani asusun daban a matsayin “kudin tallafin da aka ajiye” ba, sai dai sun wakilci karin damar kashe kudi da aka samu a tsarin rabon kudaden tarayya.
An ce karin kudaden ya taimaka wa jihohi da kananan hukumomi wajen biyan albashi da fansho, tare da kara zuba jari a bangarorin kiwon lafiya, ilimi, tituna da sauran ayyukan more rayuwa.
A matakin tarayya kuwa, an ce sauye-sauyen sun samar da karin damar kashe kudi wajen manyan ayyukan raya kasa, ciki har da harkokin sufuri, gidaje, noma, tsaro da sauran muhimman ayyuka.
Rahoton ya ce an kashe kusan naira tiriliyan 6.47 wajen manyan ayyukan ababen more rayuwa, ciki har da titin Lagos-Calabar Coastal Highway, Sokoto-Badagry Superhighway da Trans-Sahara Superhighway.
Haka kuma, gwamnatin ta ce sama da gidaje miliyan 10 sun amfana da shirye-shiryen tallafin zamantakewa, yayin da aka ware sama da naira biliyan 400 ga wasu shirye-shiryen tallafawa al’umma, ciki har da Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya, NELFUND, Asusun Zuba Jari na Gidaje na MOFI da CREDICORP.
Gwamnatin ta kuma yi ikirarin cewa sauye-sauyen tattalin arzikin sun taimaka wajen kara kwarin gwiwar masu zuba jari, karfafa kasuwar hannayen jari da kuma kara yawan kudaden ajiyar kasashen waje.
A bangaren man fetur kuwa, gwamnatin ta ce Najeriya na shiga wani sabon yanayi sakamakon karuwar karfin tace man fetur a cikin gida.
Ta yi gargadin cewa dawo da tallafin man fetur a yanzu zai iya haifar da rashin tabbas ga masu zuba jari tare da kawo cikas ga kokarin bunkasa matatun mai na cikin gida da kuma samar da isasshen makamashi.
Gwamnatin ta kuma yi nuni da cewa Najeriya na fuskantar wani nau’in tallafin makamashi a bangaren wutar lantarki, wanda ya kashe kusan naira tiriliyan 3.14 tsakanin Yuni 2023 da Disamba 2025.
A cewar gwamnatin, sake dawo da tallafin man fetur yayin da ake ci gaba da tallafawa wutar lantarki zai kara matsin lamba kan kudaden gwamnati.
Ta ce idan aka dawo da tsohon tsarin tallafin man fetur, Najeriya na iya sake fuskantar matsalar karancin mai, hauhawar farashi, matsin lamba kan kudaden gwamnati da kuma sauran matsalolin da suka sa aka cire tallafin.
Sai dai gwamnatin ta amince cewa cire tallafin ya haifar da matsin rayuwa ga ‘yan Najeriya, tana mai cewa har yanzu akwai bukatar kara daukar matakan da za su rage radadin tattalin arziki da kuma inganta rayuwar jama’a.
Gwamnatin ta ce maimakon a mayar da tallafin, ya kamata a ci gaba da amfani da kudaden gwamnati wajen zuba jari a ilimi, kiwon lafiya, tsaro, noma, ababen more rayuwa da shirye-shiryen tallafawa masu karamin karfi.
Ta ce Najeriya ba za ta iya gina tattalin arzikin gaba ba ta hanyar komawa tsohon tsarin tallafin man fetur da ta bayyana a matsayin wanda ba zai iya dorewa ba.