Saturday, October 17, 2026
HomeLabaran Jami'ar IconicIconic Open University ta fara daukan dalibai a sabon zangon karatu da...

Iconic Open University ta fara daukan dalibai a sabon zangon karatu da zai fara a Satumba

Jami’ar Iconic ta bude sabbin gurabun daukar dalibai da zai fara a watan Satumba na shekarar 2026. Dalibai masu son shiga za su iya fara cike fom domin neman gurabu a kwasa-kwasan digirin farko da na biyu da suka samu amincewar Hukumar Jami’o’in ta Kasa (NUC).

Jami’ar tana ba da kwasa-kwasan digiri na farko wadanda suka hada da:

  • B.Sc. Accounting
  • B.Sc. Business Administration
  • B.Sc. Public Administration
  • B.Sc. Mass Communication (
  • B.Sc. Computer & Information Technology
  • B.Sc. Software Engineering
  • B.Sc. Public Health (
  • B.CHS. Community Health Science
  • B.N.Sc. Nursing Science
  • B.HIM. Health Information Management
  • Doctor of Physiotherapy
  • B.Sc. Criminology & Security Studies
  • B.Sc. International Relations & Diplomacy
  • B.Ed. Educational Management da dai sauran su

Kwasa-kwasan digiri na biyu sun hada da Master of Business Administration (MBA) tare da kwarewa a fannonin banki, da kasuwancin bankin Musulunci, da Kasuwancin Man Fetur, da sauransu.

Master of Public Administration (MPA) ya shafi Manufofin Gwamnati, Shugabanci, da Ci gaban Tattalin Arziki.

Haka zalika, kwasa-kwasan digiri na biyu sun kunshi Master of Information Technology (MIT) wanda ya hada da fannonin AI da Tsaron Intanet, Master of Security Studies (MSS), Master of International Relations (MIR), Master of Public Health (MPH), da Master of Education (M.Ed.), tare da kwasa-kwasan difloma na gaba da digiri watau postgraduate diploma.

Jami’ar Iconic ta bambanta kanta ta hanyar kyakyawan tsarin karatu daga nesa (ODL), wanda ta ke da cibiyoyin jarrabawa a cikin gida da wajen Nijeriya, wanda ke bawa dalibai damar yin karatu a ko’ina ba tare da kawo cikas ga aiki ko al’amuran iyali ba.

Wata babbar fa’ida ita ce, ba a buƙatar jarrabawar JAMB/UTME don shiga ga sabbin dalibai. Bugu da kari, masu riƙe da HND/ND/NCE za su iya shiga kai tsaye cikin shirye-shiryen 200 ko 300 tare da kiredit biyar kacal a takardar shaidar SSCE.

Ga masu sha’awar neman gurbin karatu an Iconic University za su iya ziyartar yanar gizon jami’ar a www.iconicuniversity.edu.ng domin cike fom ko kuma a kira lambar waya 08142829382.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments