Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiIconic University ta kara zamanantar da shafinta na yanar gizo

Iconic University ta kara zamanantar da shafinta na yanar gizo

Jami’ar Iconic ta kaddamar da sabon fasalin shafinta na yanar gizo, a wani mataki da ta ce na daga cikin ƙoƙarinta na ƙara inganta kasancewarta a duniyar zamani da kuma sauƙaƙa wa jama’a samun bayanai game da jami’ar ta intanet.

Jami’ar ta ce sabon shafin nata an tsara shi ne cikin salo na zamani, mai kayatarwa da sauƙin amfani, wanda ke nuna tsari, manufofi da kuma matsayin jami’ar a fannin ilimi.

A cewar Sashen Bunƙasa Manhajoji na jami’ar, sabon shafin ba wai kawai wurin sanya bayanai ba ne, yana matsayin fuskar jami’ar a duniyar intanet, kasancewar shi ne hanyar farko da mutane da dama ke amfani da ita wajen sanin jami’ar.

Shafin ya ƙunshi muhimman bayanai game da jami’ar, tsarin karatunta, muhallin karatu da kuma shirye-shiryenta na gaba.

Haka kuma, an sauƙaƙa yadda ɗalibai, masu sha’awar neman gurbin karatu, ma’aikata da sauran jama’a za su samu bayanan da suke nema.

Jami’ar ta ce sabunta shafin na daga cikin matakan da take ɗauka wajen ƙarfafa kirkire-kirkire da kuma tabbatar da cewa ta ci gaba da kasancewa cikin manyan jami’o’in buɗaɗɗen karatu masu zaman kansu.

Jami’ar ta ce: “A Iconic University, ba wai kawai muna bin sawun makomar gaba ba ne; muna taka rawa wajen gina ta.”

Jami’ar ta kuma yi kira ga ɗalibanta da sauran mambobin al’ummarta, waɗanda aka fi sani da “Icons”, da sauran masu ziyartar shafin da su shiga sabon shafin domin ganin sabon salo da sauye-sauyen da aka kawo.

Sashen Bunƙasa Manhajoji na jami’ar ya ce sabunta shafin na ƙara nuna ƙudurin jami’ar na samar da ingantacciyar fuska ta zamani a duniyar dijital.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments