Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata, 25 ga Agusta 2026, a matsayin ranar hutu ta kasa domin bikin Eid ul-Mawlud, wato zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya, cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani, ta fitar ranar Juma’a.
Ministan ya taya Musulman Najeriya da sauran al’ummar Musulmi na duniya murnar wannan rana, tare da kira ga ‘yan kasa da su yi tunani kan darussan tausayi, tawali’u da taimakon al’umma da rayuwar Annabi Muhammad (SAW) ta kunsa.
Tunji-Ojo ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da lokacin wajen yin addu’ar samun zaman lafiya, hadin kai da ci gaba a kasar.
Ya ce kiyaye zaman lafiya da hadin kan Najeriya nauyi ne da ya rataya a kan kowa, tare da kira ga jama’a da su gudanar da bikin cikin natsuwa, mutunta juna da kauce wa duk wani abu da zai iya kawo rashin jituwa.
Ministan ya sake jaddada kudurin gwamnatin tarayya na ci gaba da daukar matakan kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya tare da karfafa zaman lafiya a fadin kasar.