Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare ta Yammacin Afirka (WAEC) ta sanar da riƙe sakamakon ɗalibai 167,486 da suka rubuta jarabawar WASSCE ta shekarar 2026 da aka gudanar ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa (CBT), bisa zargin aikata magudin jarabawa.
A cewar hukumar, adadin ya kai kashi 8.59 cikin 100 na jimillar waɗanda suka rubuta jarabawar bana, kuma ya nuna raguwa idan aka kwatanta da kashi 9.7 cikin 100 da aka samu a shekarar 2025.
Shugaban Ofishin WAEC na Najeriya, Dakta Amos Dangut, ne ya bayyana hakan yayin da yake sanar da fitar da sakamakon jarabawar a Legas ranar Laraba.
Ya bayyana cewa an riƙe sakamakon ne saboda zargin laifuffuka daban-daban, ciki har da amfani da wayoyin hannu a ɗakunan jarabawa duk da haramcin hakan, da kuma zargin shirya magudin jarabawa a wasu cibiyoyin rubuta jarabawa.
Dangut ya tabbatar da cewa hukumar za ta gudanar da bincike kan dukkan waɗanda ake zargi kafin ɗaukar matakin da ya dace bisa ƙa’idojin WAEC.