Sunday, October 18, 2026
HomeIlimiSama da ɗalibai miliyan ɗaya sun ci jarabawar WAEC ta 2026

Sama da ɗalibai miliyan ɗaya sun ci jarabawar WAEC ta 2026

Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Makarantar Sakandare ta Yammacin Afirka (WAEC) ta bayyana cewa ɗalibai 1,200,514 sun samu kiredit a ƙalla darussa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi, a jarabawar shekarar 2026.

A cewar hukumar, wannan adadi ya kai kashi 61.54 cikin 100 na ɗalibai 1,950,726 da suka rubuta jarabawar a faɗin Najeriya.

Sai dai WAEC ta ce ta dakatar da fitar da sakamakon ɗalibai 167,486 saboda zargin aikata laifukan satar jarabawa, yayin da ba ta bayyana adadin waɗanda ba su yi nasara ba.

Hukumar ta sanar da cewa an fitar da sakamakon jarabawar, tare da umartar ɗalibai su samar da PIN da Serial Number daga shafinta kafin su iya duba sakamakonsu ta yanar gizo.

Haka kuma, WAEC ta ce ɗalibai za su yi amfani da lambar jarabawarsu da kuma Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) da suka yi amfani da ita lokacin rajista domin tabbatar da bayanansu.

Jarabawar ta gudana ne tsakanin 21 ga Afrilu zuwa 19 ga Yunin 2026, inda kusan ɗalibai miliyan 1.96 daga makarantu sama da 24,200 a faɗin Najeriya suka halarta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments