Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Asibitoci Masu Zaman Kansu (PHIMA), Cibiyar Yaƙi da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC) da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya reshen Kano, sun kama wasu da ake zargi da gudanar da haramtacciyar hidimar lafiya a unguwar Panshekara da ke ƙaramar hukumar Kumbotso.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce an kai samamen ne bayan samun sahihan bayanai daga wasu jama’a masu kishin ƙasa kan bayar da maganin ba tare da izini ba.
“Mun ɗauki mataki cikin gaggawa da muka samu rahoton. Tawaga daga Ma’aikatar Lafiya, PHIMA da KNCDC ta je wurin tare da kama waɗanda ake zargi. Daga nan kuma muka tuntuɓi Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, kuma yanzu haka waɗanda ake zargin suna tsare a hedikwatar rundunar da ke Bompai domin ci gaba da bincike,” in ji shi.
Dakta Yusuf ya bayyana cewa waɗanda ake zargin suna gudanar da aikin ne da sunan Brother Paul Legacy Foundation, wata ƙungiya mai zaman kanta da suke ikirarin ta su ce, inda suke rarraba katinan rajista masu ɗauke da sunan ƙungiyar tare da karɓar kuɗi daga jama’a da sunan ba su magani.
Ya ce binciken farko da jami’an Ma’aikatar Lafiya, PHIMA da KNCDC suka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin shi ne jagoran lamarin tare da sauran mutanen ba ƙwararrun ma’aikatan lafiya ba ne, kuma ba su da wata shaidar ƙwarewa da aka amince da ita a fannin lafiya.
A cewarsa, katinan rajistar da suke rabawa na ɗauke da adireshi a Ƙaramar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa, kuma suna ɗauke da alƙawarin ba da “magani kyauta” domin jan hankalin jama’a su faɗa tarkonsu.
Kwamishinan ya buƙaci al’ummar Kano su guji neman magani wajen mutanen da ba su da lasisi ko kuma masu kiran kansu masu ba da magani ba tare da izini ba.
Ya jaddada cewa ya kamata a rika neman kulawar lafiya ne kawai a cibiyoyin kiwon lafiya da gwamnati ta amince da su da kuma wajen ƙwararrun ma’aikatan lafiya masu lasisi.
Ya kuma yabawa Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Alhaji Ibrahim Bakori, bisa saurin ɗaukar mataki, tare da yabawa mutanen da suka bayar da bayanin da ya kai ga samun nasarar gudanar da samamen.
Dakta Yusuf ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da kai rahoton duk wani abin da suka gani da ya shafi haramtattun ayyukan lafiya ga hukumomin da suka dace, yana mai jaddada kudirin Gwamnatin Jihar Kano na kawar da masu yin aikin lafiya ba bisa ƙa’ida ba, kare rayukan jama’a da tabbatar da cewa ana gudanar da ayyukan lafiya cikin aminci, da’a da bin ƙa’idodi.